Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ki ganawa da wakilan musamman na shugaban Afrika ta Kudu

Tinubu ya ki ganawa da wakilan musamman na shugaban Afrika ta Kudu

Rahotanni sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai gana da tawagar wakilan musamman ta Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, bayan sun isa Abuja ba tare da an tsara ganawar a gaba ba.

A cewar majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa, tawagar ƙarƙashin jagorancin Ministan Hulɗa da Ƙasashen Waje na Afrika ta Kudu, Ronald Lamola, ta isa Abuja a ranar Juma’a ɗauke da saƙo daga Shugaba Ramaphosa.

Gidan talabijin na Arise News ya rawaito cewa tawagar ta nemi ganawa da Shugaba Tinubu ba tare da sanarwa ko shiri tun da farko ba, lamarin da ya sa shugaban bai karɓe su ba.

Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan hare-haren ƙyamar baƙi da ake rahoton faruwarsu a Afrika ta Kudu, inda wasu ’yan Najeriya da sauran baƙi ke fuskantar barazana.

Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da kira ga gwamnatin Pretoria da ta ɗauki matakan kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasar, tare da tabbatar da hukunta duk masu hannu a hare-haren, yayin da har yanzu ba a fitar da wata sanarwa a hukumance daga Fadar Shugaban Ƙasa kan batun ƙin ganawar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments