Gwamnatin jihar Sokoto ta ayyana Juma’a, 24 ga Yuli, 2026, a matsayin ranar hutun aiki domin bai wa ma’aikatan gwamnati da ba su yi rajistar zaɓe ba damar shiga aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR).
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar.
Gwamnan ya ce matakin na da nufin bai wa ma’aikatan gwamnati damar kammala rajistar zaɓe da karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC) kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya buƙaci dukkan ma’aikatan gwamnati da ba su yi rajista ba da su yi amfani da ranar hutun wajen kammala rajistar, domin su samu damar sauke nauyin da ke kansu na ɗan ƙasa a lokacin zaɓe.
Gwamna Aliyu ya kuma yi kira ga sauran jama’a da ba ma’aikatan gwamnati ba, musamman waɗanda suka kai shekarun da suka cancanta su yi zaɓe, da su yi amfani da ƙarin makonni biyu da aka ba wa aikin rajistar.
A cewar gwamnan, ana sa ran za a kammala aikin rajistar masu zaɓe a ranar Lahadi, 26 ga Yuli, 2026.