Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamna Seyi Makinde ta miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa yayin hutun shekara

Gwamna Seyi Makinde ta miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa yayin hutun shekara

Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta amince da buƙatar Gwamna Seyi Makinde na tafiya hutun shekara, wanda zai fara daga 10 ga Agustan 2026.

Bayan amincewar majalisar, gwamnan ya miƙa ragamar tafiyar da harkokin gwamnatin jihar ga mataimakinsa, Bayo Lawal, wanda zai kasance mukaddashin gwamna har zuwa lokacin da Makinde zai dawo bakin aiki.

Rahotanni sun nuna cewa hutun gwamnan zai ƙare ne a ranar 11 ga Satumban 2026, yayin da ake sa ran zai koma bakin aiki a hukumance ranar 14 ga Satumba.

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Oyo sun bayyana kwarin gwiwarsu cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba tare da wata tangarda ba a lokacin hutun gwamnan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments