Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaGanduje ya soki shirin Kwankwaso na tattaunawa da ’yan bindiga

Ganduje ya soki shirin Kwankwaso na tattaunawa da ’yan bindiga

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa tattaunawa da ’yan bindiga ba ita ce hanyar da ta dace wajen magance matsalar tsaro a Najeriya ba.

Ganduje ya yi wannan bayani ne yayin wani taron manema labarai, inda ya mayar da martani ga kalaman mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya ce shi da Peter Obi za su tattauna da ‘yan ta’adda idan suka samu nasara a zaɓen 2027.

A cewar Ganduje, duk wata yarjejeniya da ake yi da ’yan bindiga na iya ƙara musu ƙarfi ta hanyar ba su kuɗi da kayan aiki, lamarin da zai iya ƙara tsananta matsalar rashin tsaro.

“Ban yarda da tsarin zama da ’yan bindiga domin yin sulhu da su ba,” in ji Ganduje.

Ya kuma bayyana cewa mallakar bindiga ba tare da izini ba laifi ne a Najeriya, don haka bai ga dacewar gayyatar masu ɗauke da makamai domin tattaunawa ba.

Ganduje ya ƙara da cewa irin wannan tsari ya taɓa gwadawa a baya amma bai samar da mafita ba.

A cewarsa, bai kamata gwamnati ta ɗauki matakan da za su iya ƙarfafa masu aikata laifuffuka ko ba su damar ci gaba da ayyukansu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments