Shugaban Cambodian, Hun Sen, ya ce dakarunsa sun mayar da martani cikin daren jiya da kuma safiyar yau Talata akan harin da aka kai musu.
Ya ce Cambodia na faɗa ne domin kare kanta bayan haƙurin da ta yi kan harin da aka kai mata a baya.
Thailand ta ce jiragenta na yaƙi sun kai hari kan wuraren da sojojin Cambodia suke, tana mai cewa manufar hakan shi ne karya lagon sojojin Cambodia.
Kawo ya zuwa yanzu dukkan ƙasashen na zargin juna da fara takalar faɗan sannan kuma kowanne a cikinsu yanzu haka na kai wa juna hari.
Aƙalla fararen hula bakwai da kuma sojan Thailand daya ne aka kashe a yayin faɗan.