Dakarun Operation Whirl Stroke (OPWS) tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai na jihar Benue sun kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne mutum biyu tare da ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a wasu hare-hare daban-daban da suka kai a jihar Benue. Hakan ya biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai bayan samun sahihan bayanan sirri kan maboyar maharan.
A cewar wata sanarwa da jami’an rundunar suka fitar, dakarun sun kutsa cikin maboyar ’yan bindigar inda suka yi musayar wuta da su. A yayin artabun, an kashe mutum biyu daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bindiga zuwa cikin daji.
Bayan kammala aikin, jami’an tsaron sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su ba tare da sun samu munanan raunuka ba. An kuma kwato wasu makamai da alburusai da sauran kayayyakin da ake zargin na ’yan bindigar ne.
Rundunar ta bayyana cewa waɗanda aka ceto an miƙa su ga hukumomin da suka dace domin a duba lafiyarsu kafin a haɗa su da iyalansu. Ta kuma jaddada cewa hare-haren da take kai wa maboyar masu aikata laifuka za su ci gaba har sai an murƙushe ayyukan ’yan bindiga a yankin.
Operation Whirl Stroke ta buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri kan motsin masu aikata laifuka, tana mai tabbatar da cewa haɗin kan jama’a na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar Benue da sauran yankunan Arewa ta Tsakiya.