Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSpain ko Argentina, wa zai zama zakaran duniya a daren yau?

Spain ko Argentina, wa zai zama zakaran duniya a daren yau?

Duniya za ta zuba ido a daren yau yayin da ƙasashen Spain da Argentina za su fafata a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026. Wasan zai haɗa manyan ƙungiyoyi biyu da suka nuna bajinta tun daga farkon gasar har zuwa kai wa wannan mataki.

Duniya za ta zuba ido a daren yau yayin da ƙasashen Spain da Argentina za su fafata a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026. Wasan zai haɗa manyan ƙungiyoyi biyu da suka nuna bajinta tun daga farkon gasar har zuwa kai wa wannan mataki.

Spain ta isa wasan ƙarshe ne bayan ta doke Faransa da ci 2-0 a wasan kusa da na ƙarshe, inda ta nuna ƙwarewa a tsakiya da kuma ƙarfi a ɓangaren tsaro. A gefe guda kuma, mai riƙe da kambun duniya Argentina ta kai wasan ƙarshe bayan ta doke Ingila da ci 2-1, bayan dawowa daga baya a ƙarshen wasan.

Masu sha’awar ƙwallon ƙafa na sa ran za a ga fafatawa mai zafi tsakanin taurarin ƙungiyoyin biyu. Ana sa ran Lionel Messi zai jagoranci Argentina a ƙoƙarinta na kare kambun da ta lashe a 2022, yayin da Spain za ta nemi ɗaga kofin duniya karo na biyu a tarihinta.

Masana ƙwallon ƙafa na hasashen cewa wasan zai kasance mai cike da dabaru da ƙwarewa, domin ƙungiyoyin biyu sun nuna ingantaccen tsari, ƙarfi a tsaron baya da kuma tasiri a kai hare-hare a duk tsawon gasar. Duk want ƙaramin kuskure na iya zama sanadin lashe kofin duniya.

Yayin da miliyoyin magoya baya a faɗin duniya ke jiran busar farkon wasan, tambayar da ta rage ita ce: shin Argentina za ta ci gaba da mulkin duniya ta hanyar kare kambunta, ko kuwa Spain za ta dawo kan kololuwar ƙwallon ƙafa ta duniya bayan shekaru 16 da lashe kofinta na farko?

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments