Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroSojoji sun dakile yunƙurin sace ɗalibai mata a Borno, sun ceto 46

Sojoji sun dakile yunƙurin sace ɗalibai mata a Borno, sun ceto 46

Dakarun rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun samu nasarar dakile wani yunƙuri na sace ɗalibai mata a Kwalejin Tarayya ta Mata da ke Monguno, a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun bayanan sirri, lamarin da ya ba su damar hana harin da kuma ceto ɗalibai mata 46 ba tare da sun shiga hannun masu garkuwa ba.

An ce matakin ya kasance wani ɓangare na ci gaba da ayyukan sojoji na tabbatar da tsaro da kare cibiyoyin ilimi daga hare-haren masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.

Hukumomin tsaro sun jaddada cewa za su ci gaba da ƙarfafa sintiri da tattara bayanan sirri domin hana duk wani yunƙurin kai hari kan makarantu da sauran wuraren jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments