Iran ta gargaɗi Amurka cewa za ta fuskanci martani mafi tsanani fiye da wanda aka gani a yaƙe-yaƙen baya idan ta ci gaba da kai hare-hare kan ƙasar.
Barazanar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kwamandan Hedkwatar Tsakiya ta Khatam al-Anbiya, Ali Abdullahi, ya fitar, inda ya ce rundunonin sojin Iran sun shirya tsaf domin kare ƙasar daga duk wata barazana.
A cewarsa, duk wani hari da Amurka za ta kai zai gamu da martani mai ƙarfi, yana mai jaddada cewa Iran ba za ta ja da baya ba wajen kare ’yancinta da tsaron ƙasarta.
Ali Abdullahi ya kuma yi kira ga rundunonin tsaro, gwamnati da al’ummar Iran da su ci gaba da haɗa kai wajen fuskantar duk wata barazana daga ƙasashen waje.
Furucin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ɗaukar sabon salo, lamarin da ke ƙara tayar da hankula a yankin Gabas ta Tsakiya.