Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeSaudiyya na shirin samar da jirgin ƙasan da zai je Qatar daga...

Saudiyya na shirin samar da jirgin ƙasan da zai je Qatar daga kasarta a awa 2

Kasar saudiyya za ta samar da jirgin kasan da zai je Qatar daga kasar a cikin awa 2

Ƙasashen Saudiyya da Qatar sun sanya hannu a yarjejeniyar fara aikin samar da jirgin ƙasa da zai riƙa sufurin fasinja a tsakanin biranen ƙasashen biyu.

Ana dai ganin wanna sabuwar yarjejeniyar da kuma aikin da za a yi zai ƙara gyara alaƙa tsakanin ƙasashen na Larabawa masu arziki.

Kafar yada labarai ta gwamnatin Saudiyya ta ce jirgin ƙasan zai iya yin tafiyar sama da kilomita 300 a awa ɗaya, inda fasinjoji za su isa Riyadh daga Doha ko kuma daga Doha zuwa Riyadh a cikin awa biyu kacal.

Kamfanonin da za su yi aikin sun ce aikin zai ci kimanin shekaru shida ana yi.

A baya dai ƙasashen biyu sun kasance cikin takun-saƙa, inda a shekarar 2017 ne dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashe biyu bayan Saudiyya ta zargi Qatar da zama ta kusa da Iran da taimaka mata wajen goyon bayan ƙungiyoyi masu zafin addini.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments