Rundunar ECOWAS ɗauke da dakarun ƙasashe 4 na yammacin Afrika ta fara aiki a Jamhruiyyar Benin kwanaki 2 bayan nasarar dakatar da yunƙurin juyin mulkin da wasu tsirarun sojojin ƙasar suka jagoranta.
Sojojin sun bayyana dalilai na ta’azzarar matsalolin tsaro a matsayin hujjarsu na yunƙurin kifar da gwamnatin Patrice Talon.
Sojoji daga ƙasashen Ghana, Najeriya, Saliyo da kuma Ivory Coast ne suka isa Benin, a wani yanayi na shirin ko ta kwana da nufin kai ɗauki ga gwamnatin ƙasar bayan daƙile yunƙurin juyin mulkin gwamnatin farar hula ƙarƙashin demokarɗiyya.
Yunƙurin juyin mulkin na Benin na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan faruwar juyin mulki a Guinea Bissau,wacce ke daya daga cikin mambobin ƙungiyar ta ECOWAS.
Tun da fari dai, dakarun sojin saman Najeriya sun kai ɗauki Benin tare da haɗa ƙarfi da dakarun sojin ƙasar wajen daƙile yunƙurin juyin mulkin inda aka jiyo shugaban Najeriya Bola Tinubu na jinjinawa dakarun waɗanda ya ce sun yi namijin ƙoƙari kuma sun yi abin da aka tura su yi a Benin.
Baya ga dakarun na Najeriya an kuma ga wasu dakarun ƙasashen ECOWAS waɗanda suma cikin gaggawa suka isa Benin don kai ɗauki ga wannan ƙasa mai yawan jama’a sama da miliyan 14.
A ranar Lahadi ne dai aka wayi gari da ganin wasu sojoji a kafar talibijin suna sanar da juyin mulki bisa kafa hujja da tarin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar, sai dai ba a jima ba, gwamnati mai ci ta bayyana nasarar daƙile masu yunƙurin waɗanda ta ce tuni ta kame su kuma suna tsare don fuskantar hukunci.