Shugaban hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado, ya yi gargadin cewa duk da kasancewa shekara guda da hambarar da gwamnatin shugaba Assad a Syria, har yanzu kasar na bukatar agajin daya kamata a ce duniya ta mayar da hankali a kai wajen taimaka mata.
Filippo Grandi, ya bayyana cewa, kasar ta Syria na matukar bukatar taimakon kasashen duniya da ma kulawarsu domin ta warke daga matsalolin da ta fuskanta a baya.
Rahotanni sun bayyana cewa al’ummar Syria a matsayin masu hakuri da juriya to amma idan har ba a inganta rayuwarsu ba, ya yi fargabar cewar za a sake barinsu cikin tagayyara.
Ya ce idan har ba a inganta rayuwar ‘yan gudun hijirar Syria miliyan uku ba da kuma tabbatar da mayar da wadanda suka rasa muhallansu da gidajensu ba to akwai sauran rina a kaba.