Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu ta hana FRSC tsayar da direbobi a hanyoyin Jiha a Kano...

Kotu ta hana FRSC tsayar da direbobi a hanyoyin Jiha a Kano baki daya

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ba ta da ikon gudanar da ayyukanta a kan hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi a jihar Kano.

Mai shari’a M. S. Shuaibu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 16 ga Yulin 2026, bayan sauraron ƙarar da lauya Abba Hikima ya shigar kan hukumar FRSC.

Kotun ta bayyana cewa jami’an FRSC sun wuce iyakokin ikon da doka ta ba su lokacin da suka riƙa tsayar da direbobi, suna neman lasisin tuƙi da yi musu tambayoyi a hanyoyin cikin birnin Kano a watan Yulin 2025.

A cewar kotun, irin waɗannan matakai sun saɓa da haƙƙin walwala da ’yancin zirga-zirga da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya tanada.

Saboda haka, kotun ta umarci FRSC da ta daina tsayar ko takura wa direbobi a hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi ba tare da hurumin doka ba.

Haka kuma, ta umarci hukumar da ta wallafa takardar neman afuwar jama’a a wata jaridar ƙasa, sannan ta biya mai ƙarar, Abba Hikima, diyyar N800,000 tare da kuɗin shari’a.

Lauya Abba Hikima ya shigar da ƙarar ne bayan ya yi zargin cewa jami’an FRSC sun take masa haƙƙinsa lokacin da suka tsayar da shi tare da neman lasisin tuƙi ba tare da ya aikata wani laifin zirga-zirga ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments