Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, sun yi kira da a ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya domin tabbatar da dorewar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.
A cewar rahoton Daily Trust, jagororin biyu sun bayyana cewa bin doka da oda, gudanar da sahihin zaɓe, inganta dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyun siyasa da kuma rungumar siyasar akida su ne ginshiƙan da za su ƙara wa jama’a amincewa da tsarin siyasar ƙasar.
Sun jaddada cewa ƙarfafa waɗannan muhimman fannoni zai taimaka wajen tabbatar da zaɓe mai inganci da zaman lafiya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Sun kuma buƙaci masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen kare dimokuraɗiyya da tabbatar da cewa tsarin siyasa ya kasance mai gaskiya, adalci da haɗin kai.