Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, wa’adin ƙarshe kan gabatar da hujjojin kare kansa a shari’ar da ake tuhumarsa da ɓata sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hanyar rubuce-rubuce da ya wallafa a shafukan Facebook da X.
A cewar rahoton Punch, Mai Shari’a Mohammed Umar ya bayyana cewa kotun ba za ta ci gaba da amincewa da jinkiri ba.
Ya gargadi cewa idan Sowore ko lauyansa suka sake kasa gabatar da hujjojin kare kai a zaman kotu na gaba, kotun za ta rufe ɓangaren kariya tare da ci gaba da sauraron shari’ar.
Kotun ta dage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 22 ga Yuli, domin bai wa ɓangaren Sowore damar gabatar da hujjojin kare kansa kan zargin da ake masa.
Ana zargin Sowore da wallafa saƙonnin da suka ɓata sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shafukansa na Facebook da X, zargin da yake fuskanta a gaban kotu.