Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai mummunan hari a kasuwar Afor da ke Nawfia, inda ake zargin mutane da dama sun mutu.
Shaidun gani da ido sun ce maharan sun bude wuta ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsananin tsoro da rudani.
Shugabannin al’umma sun tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga hukumomi da su kara tsaro domin hana aukuwar irin haka a nan gaba
Rahotanni sun bayyana cewa farmakin ya jefa mazauna yankin cikin tsananin firgici, inda wasu suka mutu a wurin, wasu kuma suka tsere domin ceton rayukansu.
Shugaban kungiyar Nawfia ‘Progressive Union’, Cif Daniel Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumomin tsaro sun fara bincike kan lamarin.