Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan daƙile juyin mulki a Benin

Tinubu ya yaba wa sojojin Najeriya kan daƙile juyin mulki a Benin

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjina wa sojojin ƙasarsa bisa jarumtar da suka nuna cikin hanzari a ranar Lahadi wajen hana yunkurin juyin mulki a ƙasar Benin

A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ƙasa ya fitar, yadda Shugaba Tinubu ya ce “sojojin sun hanzarta wajen mayar da martani game da buƙatar da gwamnatin Benin ta miƙa kan ceto dimokuraɗiyyar kasar ta shekara 35.”

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya ɗauki matakin bayan gwamnatin Benin ta buƙaci hakan sau biyu.

“Tun da fari Tinubu ya umarci jiragen yaƙin sojojin saman Najeriya da su shiga ƙasar Benin don taimakawa wajen daƙile iƙararin juyin mulkin” in ji sanarwar.

“A buƙata ta biyu kuma hukumomin Benin sun buƙaci yin amfani da kayan aikin rundunar sojin sama ta Najeriya wajen tattara bayanai da kai agajin gaggawa bisa jagorancin hukumomin Benin.”

Kazalika gwamnatin Benin ta buƙaci dakarun ƙasa na Najeriya su “aiwatar da ayyuka bisa umarnin hukumomin Benin domin kare hukumomin da ke ƙarƙashin kundin tsarin mulki tare da daƙile ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments