Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn kama wata mata bisa zargin kai wa yan bindiga miyagun kwayoyi...

An kama wata mata bisa zargin kai wa yan bindiga miyagun kwayoyi a Jihar Borno

Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation HADIN KAI sun kama wata mata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi daga wata ƙasa zuwa Najeriya, tare da ƙwace tarin miyagun ƙwayoyi, giya da sauran kayayyakin da aka haramta, waɗanda ake zargin an nufi kai wa mayaƙan ƴan ta’adda a yankin Tsibiran Tafkin Chadi.

An kama matar ne a ranar Alhamis, 9 ga Yuli, 2026, yayin da take kan hanyarta zuwa Kwatan Doron Baga a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Rundunar ta bayyana cewa bincike na ci gaba domin gano sauran mutanen da ake zargi suna da hannu a wannan haramtacciyar safara.

Haka kuma, ta jaddada aniyarta ta ci gaba da katse duk wata hanyar da ake bi wajen kai wa ƴan ta’adda kayan tallafi, miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyakin laifi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments