Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ƙasa, Bello Bodejo, ya gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Alhamis, inda ya musanta dukkan tuhume-tuhume 12 da ake masa na zargin karkatar da kuɗi da kuma tallafa wa ta’addanci.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ce ta gurfanar da Bodejo a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo bisa zargin karkatar da dala miliyan 2.63.
Har ila yau, hukumar ta kuma zargi shugaban na Miyetti Allah da ba da tallafin kuɗi ga ayyukan ta’addanci.
A farkon zaman kotun, lauyan EFCC ya sanar da kotun cewa an tsara shari’ar ne domin a karanta wa wanda ake tuhuma ƙunshin tuhume-tuhumen da ake masa.
Lauyan Bodejo, Ahmed Raji, SAN, bai nuna adawa da hakan ba.
Bayan an karanta masa tuhume-tuhume 12 ɗin, Bello Bodejo ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Daga baya, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa wani lokaci domin ci gaba da shari’ar bisa tanadin doka.