Tuesday, October 20, 2026
HomeLabaraiDuk jami’in tsaron da ya yi jinkirin harbin ɗanbindiga za mu ɗauke...

Duk jami’in tsaron da ya yi jinkirin harbin ɗanbindiga za mu ɗauke su daya – CG Musa

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya gargaɗi jami’an tsaron ƙasar da su daina jinkiri wajen ɗaukar mataki kan ƴan bindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya, yana mai cewa duk wanda ya yi jinkiri zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Janar Musa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin rabon motocin sulke da sauran kayan aikin tsaro ga hukumomin tsaro a jihar Sokoto.

Ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da ƙarfafa rundunonin tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Ya ce duk wani jami’in tsaro da aka tura bakin aiki bai kamata ya tsaya jiran ƙarin umarni ba idan ya fuskanci ƴanbindiga ko ƴan ta’adda.

A cewarsa, wajibi ne jami’an su ɗauki matakin da ya dace cikin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Babban Hafsan Tsaron ya ƙara da cewa duk jami’in da ya ƙi ko ya yi jinkirin harbin ɗan bindiga saboda yana jiran izini, za a ɗauke shi tamkar mai haɗa kai da masu aikata laifin, kuma za a hukunta shi daidai da doka.

Sai dai Janar Musa ya jaddada cewa kayan yaƙi kaɗai ba za su kawo ƙarshen matsalar tsaro ba.

Ya ce ingantaccen bayanan sirri, haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da goyon bayan al’umma su ne ginshiƙai wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments