Aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wata guguwar iska da ta afku a garin Gashua, hedikwatar ƙaramar hukumar Bade ta Jihar Yobe.
Mazauna garin sun ce guguwar, wadda ta ɗauki kusan mintuna 30 tare da ruwan sama, ta lalata daruruwan gidaje da shaguna, tare da kifar da hasumiyoyin sadarwa da sandunan wutar lantarki, lamarin da ya bar iyalai da dama ba tare da matsuguni ba tare da jawo asarar dukiyoyi ta miliyoyin naira.
Wasu mazauna garin sun bayyana cewa wannan na daga cikin munanan bala’o’in da suka taɓa fuskanta, inda suka danganta tsananin ɓarnar da sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba, wanda suka ce ya rage kariyar dazuzzuka ke bayarwa daga iska mai ƙarfi.
Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Ibrahim Babagana Yurema, ya tabbatar da mutuwar mutum uku, yana mai cewa wasu da suka jikkata na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Gashua. Ya ƙara da cewa kusan kowane gida a garin ya fuskanci wata irin asara.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, YOSEMA ta ce ta fara tantance irin ɓarnar da guguwar ta yi, wadda ta shafi wasu sassan ƙananan hukumomin Yunusari da Bursari, tare da alƙawarin kai agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa bayan kammala tantancewa.