Monday, October 19, 2026
HomeTsaroMayaƙan ISWAP shida sun miƙa wuya a Borno – Sojojin Najeriya

Mayaƙan ISWAP shida sun miƙa wuya a Borno – Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya sun bayyana cewa aƙalla mutum shida da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne sun miƙa wuya tare da iyalansu a jihar Borno, a wani mataki da rundunar ta ce na nuna ci gaba da samun nasara a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.

Mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Captain Mohammed Goni, ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa mutanen sun fito ne daga maɓoyar mayaƙan da ke yankunan Guduf Bubayagwa da Chikide da ke tsaunukan Mandara, a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta ƙwato dalar Amurka 1,120, wayoyin salula biyu kirar Tecno da wasu kayayyaki daban-daban daga hannun waɗanda suka miƙa wuya.

Sojojin sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin samun ƙarin bayanai.

Haka kuma, sojojin sun kama wani mutum da ake zargi da samar wa mayaƙan ISWAP da Boko Haram kayayyaki a shingen bincike na Molai da ke jihar Borno.

An ce an kama wanda ake zargin ne dauke da magunguna, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments