Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta naɗa alkalin wasa ɗan ƙasar Argentina, Facundo Tello, domin jagorantar wasan daf da na kusa da na ƙarshe tsakanin Morocco da Faransa, wanda za a buga ranar Alhamis.
Tello zai jagoranci tawagar alkalan wasa baki ɗaya daga Argentina. Juan Pablo Belatti da Gabriel Chade za su kasance mataimakan alkalai, yayin da Darío Herrera zai zama alkalin wasa na huɗu. Christian Navarro kuma zai kula da fasahar VAR.
Alkalin mai shekara 44 na da gogewa a manyan gasa, kuma wannan shi ne karo na biyu da yake gudanar da wasa a gasar cin kofin duniya.
Ga magoya bayan Morocco, Tello ba sabon suna ba ne, domin shi ne alkalin da ya jagoranci wasan da Atlas Lions ta doke Portugal da ci 1-0 a wasan kusa da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.
Masu sha’awar ƙwallon ƙafa na ci gaba da jiran wannan babban fafatawa tsakanin Morocco da Faransa, yayin da ake sa ran wasan zai kasance mai cike da zafi da armashi.