Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce matsalolin tsaron kasar nan na neman gagarar Gwamnatin Tarayya.
Kwankwaso, wanda tsohon Sanata ne a majalisar dattawan kasar ya yi gargadi cewa wannan halin rashin tsaro na iya jefa haɗin kan Najeriya cikin hatsari.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana damuwarsa a shafinsa na Facebook. Ya ce gwamnati ta nuna gaza wa wajen magance barazanar ’yan bindiga, ta’addanci, rikice-rikicen kabilanci, da yawaitar rike makamai ba bisa ka’ida ba a tsakanin al’umma.
Ya kara da cewa babban abin da ke nuna wannan rauni shi ne yadda gwamnati ta yi shiru tana yarda jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai duk da rashin isasshen horo. A cewarsa, hakan ya ƙara yawaitar yaɗuwar ƙanana makamai a ƙasar.
Ana samun karuwa a kafa rundunonin siyasa — Kwankwaso
Kwankwaso ya gargadi cewa wasu ’yan siyasa na cin gajiyar wannan yanayi wurin kafa rundunonin su ta siyasa, abin da ya ce yana ƙara tabarbarewar tsaron ƙasar da tuni ya yi rauni.
Haka kuma ya nuna damuwa game da ƙaruwa a tsangwama da ware mutane bisa kabila ko yanki. A cewarsa, ’yan Najeriya da dama—musamman daga wasu yankuna—na fuskantar cin zarafi, ko ma azabtarwa.
Kwankwaso ya ce kalaman kiyayya da tsoratarwa a kafafen sada zumunta, da ke tunzuri na kabilanci da addini, na ƙara lalata haɗin kan al’umma.
Kiran Kwankwaso ya taya sabon ministan tsaro murna
Kwankwaso ya roki Gwamnatin Tarayya ta yi aiki tukuru domin dakatar da wannan mummunan yanayi kafin ya fi haka muni. Ya ce yana matuƙar damuwa da yadda makamai ke yawo cikin sauƙi a ƙasar, yana mai kira hakan abin da ba za a yarda da shi ba.
Ya kuma taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nadinsa a matsayin Ministan Tsaro, yana mai cewa yana da tabbacin cewa sabon ministan zai iya yin aiki mai kyau idan aka ba shi goyon baya.