Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu: Solar za ta taimaka wajen magance rashin wutar lantarki a Kauyukan...

Tinubu: Solar za ta taimaka wajen magance rashin wutar lantarki a Kauyukan Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ƙara amfani da makamashin hasken rana (solar) domin faɗaɗa samar da wutar lantarki ga al’ummomin da ba su da babban layin wutar lantarki na ƙasa.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin Africa Mini-Grids Programme (AMP) a Abuja, inda ya ce gwamnati na mayar da hankali kan hanyoyin samar da makamashi masu ɗorewa.

A cewarsa, amfani da tsarin samar da wuta ta hasken rana zai taimaka wajen samar da ingantacciyar lantarki ga ƙauyuka da sauran yankunan da ba su da isasshen wutar lantarki.

Ministan ya ƙara da cewa shirin na AMP wani muhimmin mataki ne na bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta, tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummomin karkara.

Ya jaddada cewa gwamnati na da burin tabbatar da cewa ’yan Najeriya da ke yankunan da ba su da haɗin wutar lantarki ta ƙasa sun samu ingantacciyar hanyar samun lantarki ta hanyar amfani da fasahar Solar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments