Ifeanyi Odili, mai neman takarar gwamnan jihar Ebonyi a ƙarƙashin PDP, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027, wa’adi guda kacal zai yi a kan mulki ba tare da neman tazarce ba.
Da yake zantawa da manema labarai a Legas, Odili ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne domin mayar da hankali kan aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban jihar cikin shekaru huɗu.
Ya ce siyasar Najeriya na sauyawa daga dogaro da jam’iyya zuwa la’akari da cancanta da irin gudunmawar ɗan takara, yana mai cewa hakan ne ya sa yake samun goyon baya daga mambobin jam’iyyu daban-daban.
Odili ya kuma yi ikirarin cewa yawan masu sauya sheƙa zuwa PDP na nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki a jihar na fuskantar ƙalubale, kuma yana da yakinin samun nasara a zaɓen 2027.