Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) ta tabbatar wa ɗalibai cewa matsalolin da suka faru yayin gudanar da jarabawar a na’ura mai kwakwalwa, Computer-Based WASSCE ta shekarar 2026 ba za su shafi sakamakonsu ba.
A wasu jihohi, ɗaliban da suka rubuta jarabawar Lissafi da Kimiyyar Noma sun yi jarabawa har cikin dare sakamakon jinkirin isowar takardun tambayoyi da littattafan amsa. WAEC ta danganta matsalar da dalilan tsaro, matsalolin sufuri da kuma rasuwar wasu ma’aikatanta a Jihar Gombe, lamarin da ya shafi ayyukanta a jihohi uku.
Shugaban WAEC na Najeriya, Dr. Amos Josiah Dangut, ya ce hukumar na da tsare-tsaren da ke magance irin waɗannan matsaloli, don haka ba za su yi tasiri ga sakamakon ɗalibai ba.
Ya kuma tabbatar da cewa za a fitar da sakamakon jarabawar CB-WASSCE ta 2026 a ranar 3 ga Agusta, amma ya yi gargaɗin cewa ɗaliban da masu ɗaukar nauyinsu ke bin WAEC bashi na iya fuskantar jinkiri har sai an biya kuɗaɗen da ake bi.
Dangut ya ƙara da cewa amfani da fasaha ya taimaka wajen rage satar amsa da maguɗin jarabawa, inda ya bayyana cewa hukumar yanzu tana da cibiyar sa ido ta yanar gizo da ke gano duk wani yunkurin maguɗi a lokacin jarabawa.
A nasa ɓangaren, Babban Sakataren Ƙungiyar Daliban Najeriya (NANS), Kwamared Oladimeji Usman, ya yaba wa WAEC, tare da buƙatar ta ci gaba da bai wa jin daɗin ɗalibai muhimmanci. Ya ce bayan koke-koken da suka yi kan jarabawar da aka rubuta cikin dare, ba su sake samun irin wannan ƙorafi daga ɗalibai ba.