Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMatatar Dangote ta sake rage farashin man fetur da N50 kan kowace...

Matatar Dangote ta sake rage farashin man fetur da N50 kan kowace lita

Matatar Dangote da ke Legas ta sanar da rage farashin sayar da man fetur ga ’yan kasuwa daga N1,125 zuwa N1,075 kan kowace lita.

Wannan ragin na naira 50 shi ne karo na biyu da matatar ta yi cikin mako guda, bayan ta taba sauke farashin daga N1,175 zuwa N1,125.

Har ila yau, matatar ta daidaita farashin loda man ta teku da na kai tsaye daga matatar zuwa N1,075 kan kowace lita, tare da tabbatar da cewa sabon farashin ya fara aiki nan take.

Baya ga rage farashin, matatar ta soke tsarin sayar da mai ta hannun wata ƙungiyar ’yan kasuwa kaɗai, inda ta buɗe damar sayen man fetur ga dukkan ’yan kasuwar da suka cika sharuddan da aka gindaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments