Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ƙaddamar da shirin horas da matasa 5,000 kan fannin lantarki

Tinubu ya ƙaddamar da shirin horas da matasa 5,000 kan fannin lantarki

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da shirin horas da matasa 5,000 kan girkawa da gyaran mitocin lantarki a ƙarƙashin Shirin Samar da Mita na Shugaban Ƙasa PMI.

Shirin mai suna The Power Force na daga cikin manufofin Renewed Hope Agenda, kuma an ƙirƙire shi ne domin bai wa matasa ƙwarewar sana’a tare da buɗe musu damar samun aikin yi a ɓangaren wutar lantarki.

Tinubu ya bayyana cewa shirin a buɗe yake ga ’yan Najeriya da suka kammala karatun sakandare, tare da ware guraben musamman ga masu yi wa ƙasa hidima NYSC.

Ya ƙara da cewa ƙara yawan gidaje da kasuwannin da ke da mita zai taimaka wajen kawo ƙarshen cajar wuta ba bisa ka’ida ba, inganta gaskiya wajen biyan kuɗin lantarki, da kuma ƙarfafa tsarin samar da wutar lantarki a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments