Amurka ta sanar da janye mafi yawan dakarunta da ke gudanar da aikin haɗin gwiwar tsaro a yankin Tafkin Chadi da ke Najeriya.
Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka a Turai da Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ta yanar gizo da aka gudanar gabanin taron shugabannin tsaro na Afirka na shekarar 2026.
A cewarsa, duk da janye sojojin, Amurka ba za ta daina tallafa wa Najeriya ba, domin za ta ci gaba da samar da bayanan sirri da sauran gudummawar tsaro domin taimakawa yaki da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.