Babban Bankin Nijeriya CBN ya soke lasisin bankunan bayar da rancen kuɗi guda 46, inda matakin ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuli, 2026.
CBN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa cewa an janye lasisin ne saboda bankunan sun gaza cika wasu muhimman ƙa’idoji da sharuddan gudanar da harkokin banki kamar yadda doka ta tanada.
Bankin ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da bin ƙa’ida, kare masu ajiyar kuɗi da kuma ƙarfafa tsarin harkokin kuɗi a ƙasar.