Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya, kuma gwamnan jihar Gombe, ya ce gano dalilan da su ka tunzura ‘yan fashin daji suka ɗauki makamai, babban abu ne a yunƙurin kawo ƙarshen rikicinsu a sassan Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa ƙungiyarsu ta amince da kafa wata hukumar haɗin gwiwa kan sha’anin tsaron jihohin Arewa, tare da ba da gudunmawar Naira miliyan dubu daya duk wata ga duk jihohin Arewa 19.
Matakan dai na cikin ƙudurorin da taron ƙungiyar jihohin Arewa ya cimma a farkon wannan mako, sanadin ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga da suka janyo sace ɗalibai da rufe makarantu a jihohi da dama.