Al’ummar Tsallatawa da ke ƙauyen Bankamawa a mazabar Goron Dutse sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki sakamakon matsanancin ƙarancin ruwan sha da suke fama da shi.
A wata sanarwa da Gorondutse Social Media Committee ta aiko wa ICONIC TIMES bayan zagayen da ta yi a yankin, ta ce ta tarar da yara da dama suna jiran ruwa a wata rijiyar da ita kaɗai ce ke hidimar daukacin al’ummar ƙauyen.
Kwamitin ya bayyana cewa, bayan tattaunawa da wasu daga cikin yaran, sun bayyana cewa rashin isasshen ruwan sha na hana su halartar makaranta.
A cewar yaran, tun daga misalin ƙarfe 9:00 na safe suke zuwa rijiyar domin jiran ruwa ya taru, lamarin da ke sa su kwashe kusan yini gaba ɗaya a wajen maimakon zuwa neman ilimi.
Sun yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su dubi halin da suke ciki tare da samar musu da ingantaccen ruwan sha domin rage musu wahala da kuma bai wa yara damar komawa makaranta.