Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince da naɗin sabbin masu ba shi shawara na musamman guda shida, manyan mataimaka na musamman guda uku, sakatarorin dindindin guda huɗu da kuma mukaddashin sakataren dindindin guda ɗaya.
A cikin sanarwar da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, an bayyana cewa sabbin masu ba gwamnan shawara na musamman sun haɗa da Garba Muhammad S/Birni, Mukhtari Bello Abdurrahman, Shi’itu M. Bello, Alhaji Tukur Sanyinna, Alhaji Abdullahi Jabo da Mamman Aliyu Salisu.
Haka kuma, an naɗa Jummai Bello Kware, Nana Mamman Nasarawa da Hon. Emmanuel Ekereke a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman (SSA).
Sannan Buhari Umar, Abdullahi B. Muhammad, Musa Muhammad da Jibril Sa’adu sun zama sabbin Sakatarorin Dindindin, yayin da aka naɗa Aliyu Magaji a matsayin Mukaddashin Sakataren Dindindin.
Sanarwar ta ce dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.