Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiEFCC ta maka shugaban Miyetti Allah a kotu kan zargin laifukan kudi...

EFCC ta maka shugaban Miyetti Allah a kotu kan zargin laifukan kudi da tsaro

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) na shirin gurfanar da shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa wasu zarge-zarge da suka hada da tallafa wa ta’addanci da kuma almundahanar kudade.

Rahotanni sun nuna cewa an shigar da tuhume-tuhume guda 12 a kansa, inda ake zarginsa da karba da mallakar kudaden kasashen waje da ake kyautata zaton sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.

A cewar EFCC, Bodejo ya karbi makudan kudade daga tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, Sa’idu Abubakar, ba tare da amfani da cibiyoyin kudi da doka ta tanada ba.

Daga cikin zarge-zargen akwai karbar dala 100,000 da dala 200,000 a tsabar kudi a watan Janairun 2022, da kuma wasu kudade masu yawa da suka hada da dala 500,000 da dala 980,000 a shekarar 2024.

Hukumar ta ce za a gurfanar da shi a kotu domin amsa wadannan tuhume-tuhume da zarar an sanya ranar fara shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments