Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta gurfanar da mutum 24 a gaban kotu bisa zarginsu da hannu a kisan wata matar aure da wasu fusatattun mutane suka yi a Maraban Jos.
Ana tuhumar su da laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, kisan kai, tayar da tarzoma da lalata dukiyoyi.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga Yulin 2026, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare waɗanda ake zargin a gidan yari.
Rundunar ’yan sanda ta kuma ce bincike na ci gaba kan fiye da mutum 100 da ake zargin suna da hannu a lamarin, tare da alƙawarin gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.