Gwamnatin Iran ta ayyana hutun kwanaki uku a birnin Tehran domin gudanar da bukukuwan jana’izar marigayi Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da taron bankwana da sallar jana’izar marigayin a ranakun 4 da 5 ga watan Yuli a Babban Masallacin Mosalla da ke Tehran.
Kwamandan dakarun IRGC mai kula da shirye-shiryen jana’izar, Hassan Hassanzadeh, ya ce za a yi jana’izar marigayin a ranar 6 ga watan Yuli, tare da dakatar da dukkan ayyukan gwamnati a lardin Tehran a tsawon kwanakin hutun.
Haka kuma, gwamnatin Iran ta sanar da cewa ranar 6 ga watan Yuli za ta kasance hutun ƙasa baki ɗaya domin bai wa al’umma damar girmama tare da yin bankwana da marigayin Ayatollah Ali Khamenei.