Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya shawarci ’yan Najeriya masu shirin zuwa Amurka da su mutunta dokokin shige da fice tare da bin duk sharuddan da ke kunshe cikin bizar da aka ba su.
Sanarwar ta bukaci masu tafiya zuwa Amurka domin karatu, aiki ko yawon buɗe ido da su guji wuce wa’adin zaman da aka amince musu da shi, tare da bin ka’idojin biza yadda ya kamata.
A cewar ofishin jakadancin, bin waɗannan ƙa’idoji na taimakawa wajen kare damar samun bizar shiga Amurka a nan gaba.