Gwamnatin Jihar Kano, ta hannun Ma’aikatar Lafiya ta jihar, ta rufe wasu cibiyoyi masu zaman kansu guda biyu da ke horas da ma’aikatan lafiya, bayan gano cewa suna gudanar da ayyukansu ba bisa ƙa’ida ba a Ƙaramar Hukumar Nasarawa.
Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da IBN SINA College of Health Science and Technology, da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology, da ke Dakata Industrial Area, kan titin Bela Road, Tsamiyar Gare, kusa da titin Mai Sikeli.
Matakin rufe cibiyoyin ya biyo bayan cikakken bincike da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar, wanda ya tabbatar da cewa makarantun ba su cika ƙa’idoji da sharuɗɗan da aka gindaya domin kafa da gudanar da cibiyoyin horar da ma’aikatan lafiya a Jihar Kano ba.
Ma’aikatar ta bayyana cewa cibiyoyin na gudanar da ayyukansu ba tare da tantancewa da amincewar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ba, sannan kuma ba su da sahalewar hukumomin ƙwararru da na sa ido da ke kula da ilimin kiwon lafiya a Najeriya.
Binciken ya kuma gano manyan matsaloli da suka haɗa da ƙarancin ƙwararrun malamai, rashin ingantattun ɗakunan karatu da kayan koyarwa, ƙarancin ababen more rayuwa, da kuma gazawa wajen bin ƙa’idojin ilimi da gudanarwa da ake buƙata domin samar da ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Haka kuma, Ma’aikatar ta ce cibiyoyin sun gaza bin ƙa’idojin ɗabi’a ta sana’a, dokokin hukumomi masu sa ido da sauran sharuɗɗan da aka tanada domin tabbatar da ingancin horo da ƙwarewar waɗanda za su yi aiki a fannin lafiya.
Da yake jawabi kan lamarin, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na kare ɗalibai, iyaye da sauran al’umma daga cibiyoyin da ke tauye ingancin ilimi da ƙa’idojin ƙwarewa. Ya ce horas da ma’aikatan lafiya dole ne ta gudana ne kawai a cibiyoyin da suka cika dukkan sharuɗɗa da ƙa’idojin hukumomin da abin ya shafa.
Daga bisani, Gwamnatin Jihar Kano ta yi gargaɗi ga masu makarantu da cibiyoyin horar da ma’aikatan lafiya a faɗin jihar da su tabbatar sun bi dukkan dokoki da ƙa’idojin da suka shafi gudanar da ayyukansu. Ta ce ci gaba da rufe cibiyoyin da ba su cika ƙa’idoji ba na daga cikin matakan tabbatar da ingantaccen ilimin kiwon lafiya, kare muradun ɗalibai, da bunƙasa ingancin ayyukan kiwon lafiya a Jihar Kano.