Tawagar bincike ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da ta kai ziyara Najeriya ta ce ba ta samu hujjar da ke nuna cewa ana kashe Kiristoci ko kuma tilasta musu barin muhallansu saboda addininsu ba.
Jagorar tawagar, Farfesa Nazila Ghanea, ta bayyana hakan bayan kammala ziyarar bincike, inda ta ce matsalar tsaron Najeriya ba ta samo asali ne daga addini ba.
Ta ce yawaitar irin waɗannan zarge-zarge na da alaƙa da gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma rashin hukunta masu aikata laifuka.
Rahoton ya jaddada cewa har yanzu jami’an tsaro na da babban ƙalubale wajen magance matsalolin tsaro da suka haɗa da kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma tilasta wa jama’a barin muhallansu.