Kasashen Kenya da Amurka sun rattaba hannu a kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta kawar da cututtuka na shekaru biyar.
Yarjejeniyar ta zama irin ta ta farko tun bayan da gwamnatin Donald Trump ta sake fasalin shirin taimakon ƙasashen waje.
An ware Dala biliyan 2.5 don yaki da cututtuka masu yaduwa a Kenya, kuma ana sa ran irin waɗannan yarjejeniyar za su faɗaɗa zuwa wasu ƙasashen Afrika da ke daidaita manufofinsu da na Trump a harkokin diflomasiyya.
Yarjejeniyar dai na da nufin ƙara gaskiya da ingancin aiki, sai dai kuma abun damuwar shi ne,h akan zai bai wa Amurka damar samun muhimman bayanai kan lafiya, ciki har da bayanan sirrin majiyyata.
Ministan lafiya na Kenya, Aden Duale, ya yi ƙoƙarin kawar da waɗannan damuwar, inda ya ce:
“Bayanan da aka haɗa ba tare da sunayen mutane ba ne kawai za a raba.”
A ranar farko da ya hau kujerar shugabanci a watan Janairu, Trump ya sanar da dakatar da wasu tallafin ga ƙasashen da ke tasowa.