Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn sauke DPO a Rivers kan zargin karɓar cin hanci

An sauke DPO a Rivers kan zargin karɓar cin hanci

Zargin cin hanci ya jawo sauke DPO daga mukaminsa a Jihar Rivers

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Rivers ya cire DPO na ofishin ‘yan sanda na Oyigbo daga mukaminsa bayan zargin cewa ya karɓi rashawar naira 500,000 tare da amfani da mukaminsa ba bisa ƙa’ida ba.

Rahotanni sun ce an ɗauki matakin ne bayan wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam ya yi zargin cewa jami’in ya karɓi kuɗin daga hannun wani da aka tsare a ofishin ’yan sanda, duk da cewa ba a bayyana wani laifi da ya aikata ba.

Ana sa ran hukumar ’yan sanda za ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments