Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba da jajircewar dakarun Sojin Nijeriya wajen ci gaba da gudanar da hare-hare kan masu aikata laifuka a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, gwamnan ya jinjinawa sojojin bayan sun kwato shanu 329 da tumaki 175 daga hannun ’yan bindiga a dajin Gambanda da ke karamar hukumar Gummi.
Hakazalika, ya yaba da gudunmawar rundunar ’yan sandan jihar, yana mai cewa kokarinsu na taimakawa wajen inganta zaman lafiya da tsaro a fadin Zamfara.