Iran ta sanar da sake rufe mashigar ruwa ta Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin safarar man fetur a duniya, tana mai danganta matakin da ci gaba da rikicin da ke addabar yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun bayyana cewa Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan Isra’ila ta ƙi janye dakarunta daga kudancin Lebanon, tare da ci gaba da kasancewar sojojin Amurka a yankin.
Mashigar Hormuz na daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen jigilar ɗanyen mai da iskar gas.
Duk wani cikas da ya shafe ta kan yi tasiri ga farashin mai da kasuwannin duniya.
Matakin na Iran ya sake ɗaga hankalin ƙasashen duniya, yayin da ake fargabar cewa rikicin na iya ƙara faɗaɗa tare da shafar tattalin arzikin ƙasashe da dama.