Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake bayyana cewa ƙasarsa ba za ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon ba, yana mai cewa matakin na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaron Isra’ila.
Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin da wasu mambobin gwamnatinsa ke sukar yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka da Iran suka cimma. Ya ce kamar yadda Isra’ila ta ce ta inganta tsaro a yankunan da ke kan iyakar Gaza, haka ma za ta tabbatar da tsaro a arewacin ƙasar.
Ya jaddada cewa sojojin Isra’ila za su ci gaba da kasancewa a yankin da ƙasar ke kira “shingen tsaro” a kudancin Lebanon, muddin hakan na da amfani ga tsaron ƙasarsu.
A nata ɓangaren, Iran ta sake nanata cewa dole ne a aiwatar da tsagaita wuta a Lebanon, tana mai cewa zaman lafiyar ƙasar na daga cikin muhimman sharuɗɗan yarjejeniyar da aka cimma.