Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGobara ta tashi a ginin Polaris Bank da ke jihar Lagos

Gobara ta tashi a ginin Polaris Bank da ke jihar Lagos

Wata gobara ta tashi a wani ginin bene mai hawa 17 da ke ɗauke da ofishin Polaris Bank a titin Broad Street da ke Lagos Island, lamarin da ya jefa ma’aikata da masu kasuwanci cikin firgici.  

Wata gobara ta tashi a wani ginin bene mai hawa 17 da ke ɗauke da ofishin Polaris Bank a titin Broad Street da ke Lagos Island, lamarin da ya jefa ma’aikata da masu kasuwanci cikin firgici.  

Rahotanni sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 11:33 na safe daga bene na uku, inda wata mota da ke ajiye ta kama da wuta. Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas sun isa wurin cikin gaggawa tare da shawo kan lamarin kafin ya bazu zuwa sauran sassan ginin.  

Daraktar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas, Margaret Adeseye, ta ce gobarar ta lalata motar da ta kama da wuta da kuma wuraren da ke kusa da ita kawai, ba tare da an samu asarar rai ko raunata kowa ba. Bayan kammala aikin kashe gobarar, an dawo da komai yadda yake a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments