Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiGwamnatin Kano ta ce za ta dauki mataki kan mutuwar daliba a...

Gwamnatin Kano ta ce za ta dauki mataki kan mutuwar daliba a St.Louis

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin da ya dace bayan kammala binciken da rundunar ‘yan sanda ke yi kan rasuwar Maimuna Salisu Yaro, wata ɗaliba ‘yar shekara 14 a Makarantar Sakandare ta St. Louis da ke Kano.

Rahotanni sun ce Maimuna, wadda ke ajin JSS2, ta rasu ne bayan wani hukunci da ake zargin an yi mata saboda zuwa makare wajen addu’a.

Rahotanni sun bayyana cewa an umarce ta ta durƙusa, daga bisani ta faɗi, inda daga baya aka tabbatar da rasuwarta.

Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa-kai ta jihar, ta bakin Sakataren Zartarwa, Baba Abubakar Umar, ta bayyana alhini kan lamarin tare da mika ta’aziyya ga iyalan marigayiyar.

Ya kuma roƙi jama’a da su kwantar da hankali yayin da bincike ke ci gaba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace da zarar an kammala binciken.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments