Ƙungiyar ‘yan adawa a Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da duk wani shirin siyasar zaɓen 2027, ya mayar da hankali wajen magance matsalolin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki, ko kuma ya sauka daga mulki.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Fred Agbedi, ya ce hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kashe-kashe sun nuna cewa ƙasar na fuskantar mummunan hali, yana mai zargin gwamnati da fifita siyasa kan rayuka da jin daɗin al’umma.
Ƴan majalisar sun kuma buƙaci gwamnati ta ƙaddamar da shirin gaggawa na watanni shida domin magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, tare da ceto mutanen da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane. Sun kuma soki abin da suka kira yunƙurin raunana jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.