Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiINEC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin soke rijistar ADC da wasu jam’iyyu

INEC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin soke rijistar ADC da wasu jam’iyyu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin da wata Babbar Kotun Tarayya ta yanke na umartar ta da ta soke rijistar wasu jam’iyyun siyasa da suka haɗa da ADC, APP, AA, AP da ZLP.

INEC ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin, tana mai neman kotun da ta sake duba batun tare da dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala sauraron ƙarar.

Bayan nazarin buƙatar da hukumar ta gabatar, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da dakatar da aiwatar da hukuncin na wucin gadi, tare da sanya ranar sauraron ƙarar domin yanke hukunci na ƙarshe.

Matakin na INEC ya sake jawo hankali kan makomar jam’iyyun da abin ya shafa, yayin da ake jiran hukuncin da kotun za ta yanke kan sahihancin umarnin soke rijistarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments