Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiJita-jitar haraji kan kamfanonin man fetur da sadarwa ba gaskiya ba ce...

Jita-jitar haraji kan kamfanonin man fetur da sadarwa ba gaskiya ba ce – Gwamnati

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta ƙaƙaba sabon haraji kan kamfanonin sadarwa da na man fetur a faɗin ƙasar.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta bayyana cewa babu wani sabon haraji da aka amince da shi a kan waɗannan fannoni, tana mai cewa rahotannin da ke yaɗuwa ba su da tushe balle makama.

Ta jaddada cewa manufofinta na tattalin arziki sun fi karkata ne wajen samar da yanayin da zai ƙarfafa zuba jari, bunƙasa kasuwanci da samar da ayyukan yi, ba tare da ɗora wa kamfanoni nauyin harajin da ba a tsara ba.

Gwamnatin ta kuma buƙaci jama’a da masu ruwa da tsaki su yi watsi da bayanan da ba su fito daga sahihan hanyoyin gwamnati ba, tare da neman su rika bibiyar sanarwar hukumomin da abin ya shafa domin samun ingantattun bayanai.

Ta ƙara da cewa duk wani sauyi da ya shafi haraji ko manufofin kuɗi za a sanar da jama’a a hukumance ta hanyoyin da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments